Aljanar fatima hausa NOVELS

Share:

NA. 👑 KING BOY ISAH 👑 👉🏽✍🏻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* ✍🏻👈🏽 *بسم الله الر حمن الر حيم* _*YABO DA GODIYA SUN TABBATA GA ALLAH MAMALAKIN KOMI DA KOWA WANDA YA DAI-DAI TA GABOBINA*_ _*TSIRA AMINCI KA DADAWA FIYAYEN HALLITA ANNABI MUHAMMAD S.A.W SHUGABAN HALITTA CIKA MAKON ANNABAWA*_ _*INA ROKON ALLAH A KAN RUBUTUN NAN DA ZAN FARA ALLAH KA IYA MINI KA BANI KAIFIN BASIRA DA HIKIMA ALLAH KASA NA RUBUTA ABUNDA ZAI AMFANE MU DUNIYA DA LAHIRA, AMIN.*_ 💃🏻 GA WATA SABOWA ZAMANI MAI YAYI SABUWA. Bazan manta da ku ba domin kun zama My blood. Bazan barku ba domin in na barku na bar kaina. Bazan ki yaban ku ba domin yaban gwani ya zama dole. Bazan hana ku ba dole in mika shi gare ku littafin baki daya sadaukarwa ne gare ku MY BLOOD duk yan Kungiyar Zamani writers association ®Z.W.A banga kamar ku ba bakwa taba nuna banbanci ❤😍 💃🏻 ```Bazan taba mantawa da ku ba masoyana a duk inda kuke alherin allah ya kai muku kuna a heat na. Bari in fara rubuto ku🤦🏻‍♂ Kash! Nawan in na fara rubuta ku bazan idasaba har karshen littafin ga ruwa biro na kadan ne. Ilove you my fans``` A Cikin kado anguwar hausawa dake babban birnin tarayya Abuja.anguwa ce mai lunguna gata da tarin bishiyoyin mangorori hankan ne yasa anguwar take da inuwoyi hakan ta haifar wa da wajen duhu dan daga ance ma karfe 6 tayi to sai an haska fitila tsabar duhu in dai ba farin wata ba. Anguwa ce mai tarin jama'a, ko ta ina ka duba mutane ne kowa na uzurinsa. Akwai masu saide-saide da yan shaguna da irin tsofafin nan masu saida kayan makulace na yara. Wata yarinya ce sanye da doguwar farar riga wacce ta koma baka dan tsabar datti, Yarinyar fara ce kallo daya zakayi mata ka gane hakan saidai dauda ta masheta baka. Gashin kanta mai tsayo ne amma rashin gyara yasa duk ya fara cicirewa tsabar datti gashi duk ya barbaje mata a fuska sai ta dage shi tukun take iya ganin gabanta. Duk mai tausayi yaga yarinya to dole tausayinsa ya lunku a kanta. Domin tayi kalar ban tausan. A hanakali take tafiya har ta isa bakin kofar wani shagon saide-saide. Bakin kofar shagon taje tayi tsaye ta dan yace gashin da ya lilube mata fuska tana kallan cikin shagon. Shi kuwa mai shagon a lokacin ya dan duka daukar wani abu. 'Da dagowar shi duka hada ido da ita sai ji yayi gabansa yayi mugun faduwa. Nana take yanayinsa ya canza kalo daya zaka mishi ka gane ya fusata ainun!, "Ke uban me zan baki iyee?, haka jiya ma kika zo kika min tsaye a kofar shago kina wani nuna min ciki da baki, gaki yau kin kuma Dawowo uban me zan miki". Dayan hannuta ta daga ta dage baki hade da nuna yatsar ta cikin bakin tukun ta sauke shi ta nuna cikin ta kamar dai yanda tayi mishi jiya. Wanda duk me hankali in ya gani zai gane tana nufin yunwa take ji tana bukatar abinci, Shima kuma kanshi ya fahimci hakan. "Kaji rainin wayo ah! Lalai wannan baki sanni bane baki san bani da mutun ci ba to wllh yau zan nuna miki, to ni ubanki ne da zaki ringa nuna min kina jin yunwa ko dan kinga jiya korar ki kawai nayi ban taba lafiyar jikin ki ba. Bari ki gani". Nan take ya juya ya dauko dorina mai baki biyu wacce take jike dai mai dan tayi zafi yasa ta a mankyada Dama saboda yara ya saye ta. Goge bulalar ya fara yi domin abun man har yanzu akwai maski duk abun nan da yake yi yake yana surutai. Wato baki san na dade banyi zalinci ba ko ni dama zalinci ai rigata ce in banyi shi ba ji nake kamar a zigidir nake". Juyowa yayi a zatansa tuni taji tsoro ta gudu ganin ya dauko bulala, amma sai yaga sabanin haka ta sake bude baki ta nuna mishi kamar yanda tayi dazun. Kara fusata yayi da sauri ya bude yar karamar kofar ta kata ko ya fito. Baiyi wata-wata ba ya fara tsula mata bulala harda riketa yana fadin, "Bari in zane ki tukun gobe ma ai sai ki dawo kaji jarababiyar yarinya ni da ba ubanki ba taya zan baki abinci" yana yi ne yana dukanta tun tana kuka a hankali har ta fara ihu! Abunda da ya jawo hankalin mutane makwabtan shagon sa kenan. Sukayo mishi can aka kwaci yarinyar shi kuwa sai masifa yake. Wai ta rainashi gobe ma ta dawo. Wani dan saurayi ne naga ya kama Yarinyar yana lalashita bai ko ji kyamar ta ba kamar yanda sauran mutanan gurin sukayi. "Yi shiru yi hakuri yarinya kinji. Haba muktar yanzu dama rashin mutuncin naka har ya kai ga haka ban sani ba?, Ai da na dauka rashin mutuncin ka da masifar bai wuce iya manya ba ashe hada yara". A cewar wanda ya kama yarinyar yana lalashi. "Eh kamalu da ba ka sani ba kuma da ji kake yi yanzu kuma gashi ka gani da idanunka iyhee! Nayi rashin mutuncin in da yanda za'ayi dani ai sai ayi mugani". Da jin haka mutanan wajen suka watse suka barsu su biyu a gun domin kowa gudu yake ya wa Muktar magana ya mai rashin kunya, Dama a wajen kamala ne kadai baya raga mishi duk rashin mutuncin shi yana tsoran kamala. "Kadai kaji kunya wallahi, yanzu wannan karamar yarinyar me tayi maka da ka dake ta?". Muktar ya wani taso da masifa kamar zai haiye kamal din, " Kai kamala ka bar ganin fa ina daga maka kafa wllh ba tsoranka nake ji ba, ya za'a yi kazo kana min maganganun banza a kan wata yarinya wacce gata nan dai kamar ma yar mahaukaciya domin wannan tafi karfin ace mata ma almajira, kawai tazo kofar shagona tana daga min baki wai yunwa jiya na koreta yauma shine ta dawo shiyasa zan zane ta gobe ma in ta dawo haka sai na zane ta". Yana gama fadar haka bai ko tsaya sauraren kamal ba ya juya ya shiga shagon shi. Kamal jin saboda ta nema abinci ne ya dake ta dan takaici bai sake cewa komai ba ya kama hannun yarinyar ya nufi gidansa da ita dake ba nisa daga nan. Yana rike da hannuntq tana binshi suka shiga gidan, matarsa Khadija tana shara a tsakar gida tana jin salamar shi ta mike tsaye tana kalanshi tana kuma kalan yarinyar. "Baby sannu da zuwa wannan fa daga ina". ta fada lokacin da take kokarin kama hannun yarinyar. Kamar rai a bace ya kwashe duk yanda akayi ya gayawa matarsa, khadija nada mutunci sosai nan take taji tausayin yarinyar da sonta a cikin ranta. Gogewa yarinyar hawaye tayi hade da cewa, "Yi hakuri kinji yan mata share hawayen ya sunanki daga ina kike". Wannan tagwayen tambayoyin ta jera mata, amma shiru yarinyar batayi magana ba sai ido da take binsu da shi. Kamal ya maimata tambayar kamar yanda matar tashi tayi amma shiru. Sun tambaye ta ya kai sau biyar amma ko umh! Bata ce ba sai idanu da take binsu da shi. "Baby inaga fa wannan yarinya kurma ce shi yasa ma bataw Muktar magana ba". "Kwarai nima nayi tunanin haka, yanzu abunda za'ayi ki taimaka ki mata wanka ki zuba mata abinci taci bari inje in sayo mata wata rigar ji kafarta ko takalmi babu bari in hado da shi". A cewar kamal domin yasan matarsa ba mai bijirewa umarninsa bane ko mi ya gindaya mata inda ba na sabawa allah bane tana iyakar kokarinta. "To baby a dawo lafiya". ta fada lokacin da ta mike shima kuma ya fita Kafin wani dan lokaci tuni khadija tayi wa yarinyar wanka ta wanke mata kai. Tsabar dauda saida ta bata kusan bokiti uku da mai tsantsami ce bazata iya ba domin ko ita tanayi tana dode hanci dan tsabar wari. Bayan ta gama wankan bata mayar mata da rigar ba wani zaninta ta dauko ta liliba mata tukun ta shigar da ita ta zuba mata abinci. Ita kuma kamar wanda ya shekara baici ba haka ta fara ci hannu baka hannu kwarya. Tana gama cin abincin sai ga kamala ya shigo da sabuwar riga da takalmi mai kyau. Ya kawo ya mikawa khadija yace "ki saka mata ni zan koma shago karki bari ta fita waje". To khadija ta ambata. Kamala ya kalli Yarinyar mamaki ne ya cika sa ganin irin kyawan da ke gare ta ashe dama tsabar datti ne. Baidai ce komai ba ya juya ya wuce. Khadija ta shafawa yarinyar mai mai kanshi tukun tasa mata kaya. Ta kuma tatara gashin kanta wuri guda tasa ribbon dinta ta daure mata kan, ta jawo ledar ta bude taga ashe doguwar riga ce mai wando harda dan gyale. Ta saka mata tukun ta mikar da ita tsaye ta tsaya ta kare mata kallo sama da kasa. Wow× Masha allah beautiful baby kenan, yarinya da shegen kyau kamar aljana. (Nasmat tace, kaji min mata me ya kawo maganar aljana kuma a nan ko dai so kike ki tunawa king) Khadija tace "bari in saka miki jan baki da hoda kina so". Lokacin tama manta da yarinyar bata magana. Bisa mamaki sai taga Yarinyar na girgiza kai alamun eh. Dan dariya taye hade da cewa "dama kina jin magna ne bakya yi". Nan ma girgiza kai tayi alamun eh, Nan fa murna da farin ciki ya cika ta. Ta kuwa fara jero mata tambayoyi kala-kala. 'Acikin tambayoyin ne ta tambayi ina ne gidan su ta nuna bata sani ba ta sake tambaya ina iyayanki nama ta nuna bata sani ba har da hawaye. Khadija ta shiga lalashi tace "daga yau na zama maman ki kin yarda". Girgiza kai tayi alamun eh Nan take khadija ta rungume ta cikin farin ciki domin allah ya zuba mata san yara kuma har yanzu allah bai bata haihuwa ba sau biyu ko ta sama cikin bari take. (😭 ayya allah sarki allah ka bawa duk mai irin wannan matsala haihuwa sister na allah ya kawo 👏🏽) Haka dai ranar Khadija ta wuni cikin farin ciki duk ina tayi yarinyar na biye da ita tuni suka yi sabo har da wasanni a tsakanin su. Da magariba haka kamala ya dawo ya tarar da su khadija ta bashi labarin duk abunda ya faru ta gaya mishi ashe tana ji magana ce bata yi. Nana shima yayi mata mgana ta gyada kai. Kamala yace "To yanzu bata magana taya zamu san sunanta?". Khadijah tace "kaji wata matsalar kuma ni nama manta in tambaye ta tun dazun. (Ta juya wajen ta) kin iya rubutu". Yarinyar ta girgiza kai alamun a'a. Kamala yace "to mu saka mata suna waleeda mana tunda dai can dama muna san sunan". Khadija tayi murmushin jindadi ta kalle ta tace,"Kin yarda sunanki waleeda?". Da sauri ta girgiza kai alamun eh tana dariya nan fararen hakoranta suka bayyana. Bayyan isha'i sunci abinci sun suka danyi kallo kadan wajen karfe goma suka tashi ita kam yarinyar tuni tayi barci ma. Khadija ta dauke ta suka nufi daki suka kwanta a tskiya suka sakata khadija saida ta kare wa yarinyar kallo da kyau tayi murmushi tayi mata kiss haka shima kamala san yarinyar ya shiga zuciyar su lokaci guda. Khadija saida ta dora wa yarinyar hannu ta dan rungume ta tukun ta fara barci. Uhmmmmm wannan kenan😊 Misali karfe 11:00pm anguwar nan shiru kake ji ba motsin mutane sai kukan tsuntsaye na saman mangwaro. Badan fitulun sola da suka haske anguwar ba da duk jarumtar ka bazaka iya bi ka wuce ta cikin wannan layin ba. Shaguna duk a kulle sai shago daya wato na Muktar shi kadai ne a bude inda sabo an saba kowa ya watse a barshi shi kadai a gurin domin sai yayi lissafi tukun yake tashi. Zaune yake yana kirga cinikin da yayi yana washe baki domin yau anyi ciniki sosai a shago. Ta wutsiyar ido ya hangi kamar wani bakin abu na tafiya a kan hanya zai gifta ta kofar shagon shi. Da sauri ya dago kai dan ganin miye amma wayam. Komawa yayi yaci gaba da lissafin sa ba'afi seconds 30 ba ya kuma ganin wani jan abun kamar mutu kuma ya nufo shagon sa. Da sauri ya sake dago kai a karo na biyu nan ma baiga komai ba. Mamaki ne ya cika shi a fili yace "Kai miye haka kuma?". Ajiye kudin yayi ya fita waje a sauri ya wa-waiga ko ina har saman bishiyoyin wajan amma shiru baiga komai ba. Hakan tasa yace a zuciya "Ba komai kawai tsorata kaina ne nayi ashe". Juyowar da yayi da niyar ya koma shago yayi tozali da abunda yasa ya kwada ihu! Hade da faduwa dan razana. Ba komai idanunsa suka gani ba sai wannan yarinyar tsaye a kan kujerar da yake zaune. Fararen kaya ne a jikinta amma gaba daya sun baci da jini wuyanta a yanke jini na zuba har tsartuwa yake yi. Idanunta kuwa sunyi jawur jini na bulbula daga ciki haka hakuranta sun kara zarowa sun fito waje jini cike da bakin. Kuma a hakan murmushi take wani irin sauti na fita kadan-kadan............. 😰 Kodai aljana ya zane 🙆🏻?? Muje zuwa Karkuyi zatan labarin Aljanar fatima ya canza ne 😀fa

1 comment: