Kamar yadda mukayi alkawarin yin bayani akan wani bala'i da ya futo na kera wata (sex dolly)'yar tsanar jima'i wacce take dauke da dukkan sifofi na mace,ta yadda namiji zai iya tarawa da ita ya fitar da maninsa,kuma wannan matar tana magana kuma tana iya fitar da sauti da zai iya daga hankalin namiji bayan kuma motsi da take iya yi bayan anyi mata caji da lantarki.sannan ana sayar da ita akan kudin da zai isheka ka auri mata biyu kimanin naira dubu dari takwas #800,000.abun bakin ciki yanzu shine yadda matasa suke rigegeniya wurin odar wannan bala'i.
Allah mai girma yace a cikin Alkurani yana sifanta muminai "sune wadanda suke kiyaye farjinsu,saidai ga matansu ko abunda hannayensu suka mallaka (kuyangu)to su ba abun zargi bane,amma duk wanda ya nemi koma bayan haka to wancanenka sune masu keta doka " (muminun)sannan Allah madaukakin sarki yace "wadanda basu sami aure ba su kame har sai Allah ya wadatasu daga falalarsa.."(Nur)
Manzon Allah yace"Ya ku jama'ar matasa Duk wanda ya samu ikon yayi aure amma wanda bazai iya ba to yayi azumi...."bukhari da Muslim.
Manyan malaman musulunci,cikinsu akwai ibnu taimiyya sun bada fatawar haramcin mutum ya (istimna'i)wato yayi anfani da hanunsa ko wani abu don fitar da maniyyi,dogaro da dalilan da suka gabata na mafita da Allah da manzonsa suka bayar akan wannan damuwar.sannan yin hakan zai kawo gudun sunnar manzon Allah domin matasa zasu nisanci aure,kuma hakan kyamar sunnan manzon Allah ne.
sannan wannan matar robar da ake saya mafi karancin kudinta dalar amurka $2000 ko fiye da haka,wanda yana daidai da naira dubu dari takwas na najeriya#800,000,wato zai iya aura maka mata biyu a takaice.
No comments