Mustapha Saddiq Wata kungiyar wadda ba ta gwamnati ba ta karrama daya daga cikin manyan malaman Izala a Najeriya watau Sheikh Ahmad Mahmoud Gumi a gidan sa dake a garin Kaduna, jihar kaduna. Wannan dai na zuwa ne a dai dai lokacin da kawunan 'yan kungiyar ta izala ya rarraba biyo bayan goyon bayan da shugabannin kungiyar suka yi wa tazarcen shugaba Muhammadu Buhari. : Wata kungiyar dake goyon bayan Atiku tayi bikin karrama Sheikh Gumi Source: Obasanjo Goyon bayan da shugabannin izalar suka yi dai wasu na ganin bai dace ba domin bai kamata malaman addini su shiga siyasa ba yayin da wasu kuma ke ganin hakan ya dace kuma yayi daidai da ra'ayin su.
No comments