MATA SAI FA MUN GYARA!👿

Share:


*

👿Wasu daga cikin dalilan da ke sanya jinnu shiga jikin mu fiye da maza. Duk wanda ya san matarsa ko 'yarsa na yi ku gyara musu:

👿1. Zama a bakin qofa, ko bakin windo da sauran hanyoyin wucewa.

👿2. Fesa turare mai qarfi yayin fita, ko kuma fesa turare lokacin kwanciya bacci mai qarfi kuma ba addu'a.

👿3. Yawan yin zanen lalle mai fulawa a madadin asalin na gargajiya. Wanda aljani da kanshi ya fad'i cewa kwalliyar su ne a jikin wata.

👿4. Zama babu ďankwali a cikin gida, da kwanciya babu shi. Ko bayyana gashin a fita waje.

👿5. Yawan zama ba tsarki, kamar in an yi an gama da dare kawai ta kwanta babu tsarki cikin qazanta. Kuma babu ko alwala har gari ya waye tangararan. 

👿6. Rashin yin alwala a lokacin jinin al'ada da barin yin dukkan addu'o'i. Mafiya yawa in tana jini sai ta yanke dukka komai har sai ta yi tsarki. Wanda hatsari ne sosai.

👿7. Yawaita fushi da sanya damuwa a rai koda yaushe. Domin wata da aljanar ta shige ta cewa ta yi kullum in ta zo wuce wa zata ga tana bakin ciki da damuwa. To wai ita ma aljanar irin halin da take ciki kenan sai ta shigeta. Idan ta na magana ita kaďai na baqin ciki sai aljanar ta rinqa amsa mata tana rarrashinta. Daga karshe dai ta shigeta, in aljanar na baqin ciki sai ta rinqa yanka jikinta da wuka. Wanda matar ma haka ta koma yi.

👿8. Caba ado na gani na fada a fita musamman ga wacce bata yin azkar. Da gyara adon in an samu wuri a waje ko a cikin mota. Domin ita ma wata a nan jinnun ya shige ta. Yace ta tsaya a titi ta fito da powder ta qara shafawa ta gyaggyara. Shi ya zo wucewa sai ya ga gaskiya yana sonta.

👿9. Zama a wuraren da aka san suna zama. Kamar wuri da koda yaushe ke da danshi, zama tsakanin inuwa da rana (rabinki a rana rabi a inuwa). Qin shiga bandaki da addu'a ko dankwali. Ko yin waqe waqe a banďaki.

👿10. Shagala da duniya da yawa. Bana manta wani Ruqya da na kalla na wani bature ďan America. Aljanu ne a jikinsa sun kai 10 wanda a dalilin badala ya samo su. Sai suka sa ya zama mutumin banza sosai. Wani daga cikin aljanin da ya shigo jikinsa aka ce shi kuma me yake sanya shi? Ya ce party 😂. Duk in da aka ce za a yi party to aljanin zai takura sa har sai ya je wurin sun gwangwaje. To kana iya gamuwa da jinnu mai irin zunubinka ko dabi'unka na sa'bo sai ya shiga, ya sanya ka yin fiye da abun da ya same ka a kai. 

👿11. Shiga kasuwa babu addu'a. Ko shiga daji ko wani wuri da babu mutane sosai ba tare da addu'a ba. Akwai wani jinnun da ake magana da shi a jikin wata yarinya akan irin halittun da yake zama. Sai yace har da kare, kadangare, maciji, da jemage. Ya ce ya taba zama kare ne ya ci ji wani mutumi bayan ya shiga daji ya taka shi. Shi kuma in an ta'ba shi baya yafiya. Aka ce ina mutumin yanzu, ya ce yana can yana wahala da ciwonsa na sa masa ciwo. Kenan in zaki shiga irin wadannan wurin sai a yi addu'a a nemi tsari daga su.

👿12. Yawon dare, fitan magriba, sharan magriba, wankan magrib. Dauko ayyuka a magriba. Domin Annabi (SAW) ya fada mana a lokacin suke barbazuwa. To in so samu ne a dan bari magriban ya gitta sai a yi. Kuma ki rinqa qoqarin kammala ayyukan ki kafin nan. Da nutsa yara.

👿13. Zubar da ruwa mai zafin gaske. In kin wanke shinkafa ko kin yi per boiling ki yi banza da shi har ya huce sai ki nemi tsari (Auzu billaahi minash shaydanir rajim) ki zubar. Saboda wurin kwata da wanke-wanke suna da danshi da qazanta. Haka nan da zubar da bola da tsakar rana musamman in akwai wani abu na glass da ya fashe a ciki. Wanda in kin watsa in akwai wani abu zai iya jin masu ciwo. Haka nan zubarwa da Magriba. 

👿14. Kashe wasu halittu a gida ba tare da kin nemi tsarin Allah ba. Babu abun da basa zama duk abun da kika gani ko zaki kashe ki nemi tsarin Allah. Bana manta ina sakandiri na kwana, wata yarinya ta kashe tsaka. Wacce ta kashe tsakan hannunta ya rike, washe gari ya kumbura. Itama wacce ta share ta hannunta ya rike sai da aka mayar da su gida.

👿15. Yin wulakanci ga mutumin da baki sani ba a hanya. Domin wannan halin mata ne. Gashi kin fita babu azkar, ga shi kin caba ado, an tare ki kuma kin yi wulakanci. Kin ga sai ya shiga jikinki da hujjah.

👿16. Barin qashin kaza ko na wani dabba yana kwana miki a daki ba tare da kin fitar ba. 

👿17. Shiga turken awaki da magriba ko yawan shiga babu azkar. Domin wurin akwai qazanta suna iya zama a wurin.

👿18. Rashin yi wa 'ya'yan mu tofi idan sun fadi musamman da Magriba. Kada ki yarda ya fadi baki karanta falaqi, Nas, Ikhlas ba ki tofa a hannun ki. Ki shafe fuskansa sannan dukkan jikinsa. Zaki iya hadawa da sauran addu'oi ma. Wata sun shigeta ne sanadiyyar fadi da tayi a bakin qofa da 'yarta sai kuma bata yi addu'a ba. Ashe aljani ta fada ma wa a bayansa, sai ya kama yar. Ta yi shekaru yana azabtar da mutanen gidan dukkan su, bama wai ita kadai ba.

👿19. Barin 'ya'yan mu su kadai suna jarirai. Kuma ba tare da mun yi musu tofi ba. Wanda yara da yawa sun girma da jinnu ne a jikinsu. Su yi ta azabtar da iyayen basu sani ba.

👿20. Zuwa diban ruwa da Magriba, musamman ga masu tsohon ciki. Ko wucewa ta qarqashin bishiyoyin da aka san aljanu na zama. Da mace mai sana'ar aiken yara da Magriba. 

👿21. Shirka da yawon gidan malamai, wanda mafiya yawan mata a nan suke debo wa. Haka nan amfani da layu, ko wasu abubuwan da aljanu suke so. Aiki da turarukan da ake kiran iska da su ko iska ke so. Kamar misalin binta Sudan. To kuwa shaidanu zasu dabaibaye miki gida da 'ya'ya. Ga bala'in shirka, ga bala'in jinnu, ga bala'in rashin samun biyan bukata.

👿22. Canza launin fatarki, qara gashi da ko wane irin abu ne, ko ruwa na shiga ko baya shiga. Shafa kwatas a qumbarki, canza kalolin gashi gasu nan dai abubuwan canza halittar Allah. Suma tabbas jinnu na shiga jikin mace ta dalilin su. 

👿23. Nisantan Allah. Yin mugunta, da zama mai baqar zuciya. Yawan jin tsoro da yawn rudewa.

👿24. Yawo na rashin dalili kullum kina tafe a hanya yana sanyawa a yi gamo.

👿25. Bayyana tsiraicinki a social media da zahiri. Domin ana gamo da aljani ta chatting. Yawan hira da mu'amala da maza shima zaki iya gamuwa da jinnu. 

👿Yan'uwana aljani gaskiya ne na san kun san da haka, kuma suna shiga jikin mutum su zauna har su haifar masa da wasu dabi'u, ciwo dss. In mutum ya qaryata toh wata kila bai faru da na kusa da shi bane ya ga zahiri. Jinnu sun yi mutukar shigowa cikin mutane yanzu. Don haka kuskure ne cewa jinnu baya shiga jikin dan adam. Domin zai sanya mutane sake da addu'a da jin cewa komai lafiya.

🤲🏼Mu rike addu'oin safiya da maraice gasu nan a Hisnul Muslim. Domin in sun kama mutum da kansa zai kore su da addu'oi. Domin in magani ne in ya qare zasu dawo. Addu'a kuma dai baya qarewa. Mu yawaita karanta qur'ani da neman tsari da su. Ya Allah Ka bamu kariya

No comments