Me daga hannun Ganduje da Buhari ya yi ke nufi?

Share:
Wasu masu sharhi kan sha'anin siyasa sun ce daga hannun gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi alama ce da ke nuna jam'iyyarsu ta APC za ta samu tagomashi a zaben 2019.

A ranar Alhamis ne shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya kai ziyarar yakin neman zabe jihar Kano.

Shugaba Buhari ya je Kano a daidai lokacin da ake takaddama a tsakanin 'yan siyasa da sauran al'umma, a ciki da wajen jihar, a kan bidiyon da ake zargin gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje da karbar rashawa.

Wasu 'yan kasar musamman 'yan hamayya na ganin Shugaba Buhari ba zai daga hannun Gwamna Ganduje ba saboda alwashin da ya sha na yaki da cin hanci da rashawa ba tare da sani ko sabo ba.

Sai dai shugaban ya daga hannun gwamnan lokacin ziyarar tasa.

   
A tattaunawarsa da BBC, Malam Kabiru Sufi da ke koyar da harkokin siyasa a Kwalejin Share Fagen Shiga Jami'a ta Kano, ya ce daga hannun Gwamna Ganduje da Shugaba Buhari ya yi tamkar ya amince da shi ne duk da babban zargin da ke wuyansa.

A cewarsa, hakan zai iya bai wa jam'iyyar APC kwarin gwiwar shiga zaben watan da muke ciki.

"Tasirin daga hannunsa shi ne zai taimakwa jam'iyyar APC wajen kai wa ga gaci a zabukan matakai daban-daban. Ta bangaren magoya baya kuwa, watakila idan a da an sa musu shakku, to zuwan nasa ya rage musu wannan

No comments