MEYASA HAMMTA DA TSAKIYAR CINYOYI SUKE BAKI?

Share:
A kan samu wasu matan masu fama da bakin hammata da cinyoyi, musamman idan suna gugar juna. Idan kina da irin wannan matsalar, share hawayenki, na tanadar muku da tsarabar musamman na magance wannan.

Abu na farko da uwargida za ta yi bayan askin gashin hammata shi ne, ta shafa man zaitun, kada ta shafa hoda, domin hoda na shanya wajen ya yi baki. Bayan an shafa zaitun din za a bar har na tsawon kwana uku. Daga nan ba za a shafa komai ba, duk sanda uwargida ta yi wanka, ba za ta kara shafawa komai ba, sai turare. A rana ta uku sai ta nika Cocumber, ta shafa ruwan a hammata, kafin ta shiga wanka. Ta bar shi har sai ya bushe, ta shiga wanka. Bayan ta fito, sai ta kara shafa zaitun din. Haka ma za a rika shafawa tsakanin cinyoyi.

A kula, bin wadannan ka’idojin yana da matukar amfani, don haka uwargida ta daure ta bi su daki-daki.

Yadda Za Ki Kiyaye Ni’ima A Jikinki

Shakka babu akwai bukatar Iyayenmu mata su san me ke kawar da Ni’imar jikinsu, kuma ina son mata su sani cewa akwai wasu matan da Ni’imar jikinsu take zubewa tun suna yara kanana, kuma da yawa daga cikin irin wadannan matan har karshen rayuwarsu Ni’imar jikinsu ba za ta taba dawowa ba. An kiyasta kashi 90 daga cikin 100 na wadannan matsaloli ana samun su ne daga rashin sani da kuma sakaci na Iyaye mata. Mu sani cewa masana suna cewa gaban mace (al’aurarta) yana saurin cafkar kwayoyin cuta ne kamar yadda mayen karfe yake cafkar karfe da zarar karfen ya kusance shi, kuma da zarar cututtuka sun yi yawa a al’aurar, to ni’imar jikinta ya rika wargajewa kenan.

Iyaye mata kusa ido ku ga wasu daga cikin abubuwan da ke haifar da wargajewar Ni’imomi a gare ku. Na farko shi ne hanyar da kuke bi wajen tsaftace yaranku, misali yarinya ta yi bayan gida, ta gama, idan za a wanke mata, to maimakon a sata ta tsuguna sosai, kawai sai dai a yi mata tsarkin ta ko wane hali. Wanda in ana wanke mata a hakan, an manta cewa ruwan daudar wannan kazantar yana tafiya kai tsaye zuwa cikin jikinta, musamman ma idan ta yi goho, zai iya komawa cikin al’aurarta, shi kuma bayan gari shi akarinkansa cuta ne wanda ya tattare wasu munanan kwayoyin cuta, don haka kun ga tun daga nan, an fara gurbata irin ni’imar da irin wadannan yara za su ta su da ita.

Abu na gaba shi ne barin yara su dinga zama ba wando a jikinsu, wannan ma yana bada gagarumar gudumawa wajen saurin kamuwa da cututtukan gaban mata. Haka nan yawan shaye-shaye ko shafe-shafen kayan karin Ni’ima musamman na Turawa ga ‘yan mata ko matan aure, shi ma yana hassada wannar matsala ta wargajewar Ni’imar cikin ‘ya mace, don da yawa a nan ne wasu matan garin neman kiba, sai su samu kansu cikin rama. Sannan uwa uba ga wani abu da ke faruwa a wajen ma’aurata mata wannan karon har da mazan ma, shi ne yadda suke amfani da kyalle ko hankacif daya wajen share ko goge najasa a yayin da aka kammala ibadar aure, wanda wasu da yawa suna ganin wai hakan yana cikin so da kaunar juna, wanda Wallahi Malamai suna cewa wannan ba kawai yana haifar da kwayar cuta ba ne, mummunar kiyayya ya ke haifarwa wanda kusan ma ba ya da magani.

Haka zalika, barin gashi ya yi yawa a matsematsin ma’aurata wato, su rika shafar junansu da shi a lokacin saduwa, shi ma yana haifar da matsala ga ma’aurata kuma yana kauda sha’awa. Malamai suka ce, wannan ne ma dalilin da ya sa aka ce namiji duk bayan kwana 40 ya aske gashin gabansa, ita kuma mace duk bayan kwana 20 ta aske nata.

Iyayenmu mata, in so samu ne ana son mace ta zamo ko a bayan daki ta bambanta wajen da take tsuguno ta yi fitsari da inda take wanka, haka nan an so mace duk lokacin da za ta yi tsarki ta samu ruwa mai tsafta sosai, in so samu ne ta yawaita yin tsarki da ruwan dumi, yin hakan yana taimakawa sosai wajen gujewa kamuwa da cututtuka da dama da kuma magance wasu cututtukan. Iyaye mata ku daina shafa duk wani mai a gabanku, duk sana gurbata Ni’imar ‘ya mace. Maimakon hakan ku samu man Zaitun ku rika shafawa a duk lokacin da kuka yi wanka ko kama ruwa musamman da ruwan zafi. A guji barin jikakken kaya a jiki masamman wandunan ciki (Pants ko Underwear), hakan shi ma yana haifar da wargajewar Ni’imar da ke jikin ‘ya mace. Sannan ku tabbatar kun goge jikinku sosai bayan kun fito daga wanka ko kama ruwa kafin ku maida kaya jikinku, kiyaye yin hakan zai taimaka gaya yajen gujewa kamuwa da cututtuka a gare ku.

Daga karshe ina mai ba ku shawara da cewa ku yawaita shan ‘ya’yan itatuwa domin karin Ni’ima gare ku, maimakom shan wasu kwayoyi da ba ku san asalinsu ba.

No comments