HUKUNCIN SHAN RUWAN MANIYYIN MIJINKI

Share:
 


SHIN YA HALATTA MUTUM YA BAWA MATARSA MANIYYINSA TA SHA, WAI YANA GYARAWA MATA JIKI?
*SHIN YA HALATTA MUTUM YA BAWA MATARSA MANIYYINSA TA SHA, WAI YANA GYARAWA MATA JIKI?*

الحمد لله.

*AMSA:* Maniyyi awajan wasu malamai Najasa ne, kamar Mazhabar Hanafiyyah sukace: Maniyyi najasa ne mai Qarfi, Ana tsarkaka daka gareshi ta hanyar wankewa da ruwa idan yana danye jiqaqqe bai bushe ba, idan kuma ya riga ya bushe idan aka kan-kareshi ya tsarkaku.

Abisa wannan Wasu Malamai sukai fatawa da haramcin shansa, saboda gujewa Abunda wasu mazhabobi sukai fatawa da shi na najasarsa.

Abisa fatawar wadanda sukace: Mai tsarkine ba najasa bane baza’a shashi ba, domin Wani yankine na dan adam, Bai halatta amfani da wani yanki na dan adam ba batare da wata lalura ba, domin yankine na wani Abu shine ruwa mai wari.

Dalilin Haramtawar shine kafin fitowar maniyyi akwai Ababen da suke zuwa kafinsa wadanda sudin najasane, kamar maziyyi da wadi galibi Sai Maziyyi ya fito sannan maniyyi yake biyo bayansa.

Sahihiyar magana itace maniyyi ba Najasa bane, Amma shansa ya danganta da wanda yaga zai iya sha, Shansa ko rashin shansa kamar Sauran Ababene dasuke halal amma saboda qyama wani bazai iya shaba wani kuma zai iya sha.

Kamar saduwa ne da mace lokacin datake jinin rashin lafiya, ya halatta mijinta yasadu da ita da wannan jinin, amma inyaga bazai iyaba shikenan, ba saboda haramun bane.

Amma Kada hakan yazama wata Al’ada abar mai-maita ko yawan aikatawa.

Sannan dole ayi duba ta fuskar su wanene galibin masu yin irin wannan dabi’ar, idan fasiqaine ko mazinata ko kafirai, to kaga Anan zai zama haramun, ba saboda shan haramun bane, a,a sai saboda koyine da kafirai mutanen banza, dolene akula da wannan.

*MENENE HUKUNCIN MA’AURATA SUJI DADI DA BAKINSU DA AL’AURAR JUNANSU (TSOTSAR AL’AURAR JUNA)?*

Miji shari’a ta bashi dama yaji dadi da matarsa yanda yaso, yaje mata ta inda take haihuwa ta kowanne guri yaso, Kamar yanda Allah yafada acikin aya ta *(223) cikin suratul Baqara.*

Abu biyu aka haramtawa miji wajan zakkewa matarsa.

Nafarko: Saduwa lokacin haila, Kamar yanda Allah yafada acikin ayata *(222) cikin suratul Baqara.*

Na Biyu: Saduwa ta dubura, Manzan Allah Sallallahu Alaihi wasallam yace: ( Tsinanne ne duk wanda yajewa matarsa ta dubura,) *Abu dawda da Ahmad suka ruwaito shi, Albani ya Ingantashi acikin Saheehu jami’i (5889).*

Duka Ababe biyun Wani hadisin Ya hadesu baki daya, Annabi Sallallahu Alaihi wasallam yace: ( Ku guji saduwa ta dubura da lokacin Haila).
*Ahmad Abu dauda suka ruwaito shi, Yana cikin jami’ussaheeh (1141).*

Tsotsar Al’aura da baki, Akwai sharudda guda biyu;

1- Yakasance hakan baya cutarwa, ko jawo cuta.

2- Kada yazama sababi na wucewar najasa zuwa maqogwaro.

Shaik Abdurrahaman yace: Ya kamata Nisantarsa dan Kunya da gujewa Abunda ke tattare dashi na qazanta da Sabawa fidra da yayi, da lura da cewa zai hana mace biyan buqatarta idan miji ya saba mata dashi.

*HUKUNCI MACE TA TARE MANIYYIN MIJINTA TA SHANYE?*

Mace ta tare maniyyin mijinta ta Shanye Bai halatta ba, saboda Abubuwa kamar haka;

@- Najasa zata iya shiga zuwa bakinta, Babu Amincin cewa maniyyi zai fita batare da wani Abu na najasa yafita tare dashi ba, Musamman farkon Maniyyi kamar Maziyyi da wadiyyi, ko fitar fitsari akarshen harbowa maniyyi, zato anan yana zama hukuncin "Mi’ina" (Yaqini) Kamar yanda malaman fiqhu suke cewa, ta wannan fuskar sai aka haramta, shari’a tazone danta toshe qofar da zatakai ga barna.

2-Koda Wasu Malamai sunce Maniyyi Mai tsarkine, To basa halasta mace ta tareshi ta shanye dan Qazantane, saboda fadin Allah madaukakin Sarki a aya ta *(157) Cikin Suratul A’araf.*

Qazantar da Abu A wajan Musulmi yana komawa zuwa ga Al’adarsu idan babu wani Nassi na shari’a dayace Qazantane ko Najasane.

A Al’adar larabawa da Musulmi tunda can mace bata aikata haka da mijinta, Al’ada Abar yin hukunci da itane kamar yanda malaman Usulu fiqu suka fada.

3- Akwai kama da kafirai acikinsa, da Mahaukata, da Mazinata wadanda burinsu kawai shine aji dadi na sha’awa, da kama da dabbobi, Annabi Sallallahu Alaihi wasallam yace: ( Wanda yai kama da Wasu mutane yana cikinsu) Ahmad da waninsa sun ruwaitoshi da Isnadi mai kyau.

Wajan Musulmi ba’asan idan Mutum ya sadu da matarsa zata tare maniyyinsa ta shanye ba, Sai a lokacinda Lalatattun Musulmai Suka fara koyi da kwai-kwayon kafirai yahudawa da Kiristoci da wasu fandararrun musulmai, Dama Annabi Sallallahu Alaihi wasallam yace: ( Zaku bi sawun wadanda suka gabaceku, qeqe da qeqe, sai Sahabbai sukace: Yahudawa da Kiriatoci, sai yace: Suwa nake nufi inba su ba.?)

Bukhari da Muslim.

Allah madaukakin Sarki yace: ( Su kafirai kamar dabbobi suke, kai sunfi ma dabba bacewa, Su din gafalallu ne).

Saika ga Bawa yana kwai-kwayon wanda yafi dabba bacewa!.

Ta wannan fuskar haramun ne, domin kamanceceniya dasu afili yake qarara, wannan bai yadu acikin musulmi ba sai bayanda, fina finai da kafafen internet na hotuna dasuke nuna yanda ake zina suka yadu tsakanin Musulmai, suna biyan buqatarsu a siffar da ko dabbobi basa yinta, Inaga Ma’abota hankali da tunani Ingantacce, da Kunya da kamewa da tsafta?!.

No comments